IQNA

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Baje Al'adunta A Baje Kolin Ghana

Bangaren al'adu da fasaha:a kasuwar baje kolin shekara shekara da asar Ghana ke gudanarwa a kasarta da ke yammacin nahiyar Afrika an samu halartar kasashe talatin na duniya da suka hallara a birnin Accra fadar mulkin kasar ta Ghana kuma jamhuriyar musulunci ta Iran tana daga cikin kasashen da suka halarci wannan kasuwar baje kolin inda ta bude dakin al'adunta.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a kasuwar baje kolin shekara shekara da asar Ghana ke gudanarwa a kasarta da ke yammacin nahiyar Afrika an samu halartar kasashe talatin na duniya da suka hallara a birnin Accra fadar mulkin kasar ta Ghana kuma jamhuriyar musulunci ta Iran tana daga cikin kasashen da suka halarci wannan kasuwar baje kolin inda ta bude dakin al'adunta. Wannan kasuwar baje kolin wata dabbar dam ace ga kasashen na nuna irin karewarsu ta fuskar al'adu da kuma sada zuminci a tsakanin kasashen da al'ummominsu daga cikin kasashen da suka halarci wannan kasuwar baje kolin akwai : Iran,Turkiya,Ghana,Labanon,Hunduras,Keniya,Nigeria,Italiya,Seraleyon,Libya,Ostriya,Lahistan,Kanada,Tailand,Malawi,Nervej,Japon,Uganda,Masar, Suriya,Zimbabwe,,Togo,Amerika,Island,Zambiya,Kuiba,Cana da Gambiya.





755923