Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Sheikh Muhammad Husein babban mia bada fata a Kudus da Palasdinu ya sanar da dakatar da yada wasu kur'anai guda biyu da aka buga saboda kuskuren shafukan da suka kumsa ba daidai suke ba.Daya daga cikin kur'anai biyu an buga shi ne a mataba'a ta Mansura da ke kasar Masar kuma ya samu amincewar jami'ar Azhar kafin bugawa amma an tsallake shafi na sattin da hudu da shafi na tisi;in da biyar saboda haka aka dakatar da bugawa.
755814