Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun an bayyana cewa, wanda ya kafa babbar jami’ar nan ta musulunci ta kasa da kasa a birtaniya Muhammad Ali Sharistani, ya rasu wata asibiti da ke birnin Tehran bayan fama da wata rshin lafiya. Da ya dauki tsawon lokaci yan afama da ita.
Za a dauki gawarsa daga birnin Tehran zuwa birnin Bagadaza na kasar Iraki, inda za a raka ta zuwa garin Kazimain, daga nan kuma za dauke ta zuwa garin Karbala mai alfarma inda za a rufe ta a can, tare da halartar malamai da kuma wasu daga cikin jami’an gwamnati ami da sauran al’umma.
Ali shahristani dai daya ne daga cikin masana addinin musulunci da ya taka gagarumar rawa ta fuskoki da dama domin ci gaban addinin muslunci a fadin duniya, daga cikin kuwa har da gagarumin aikin da ya yi na kafa babbar jami’ar muslunci ta kasa da kasa a cikin kasar Birtaniya.
Kafa babbar jami’ar nan ta musulunci ta kasa da kasa a birtaniya da Muhammad Ali Sharistani ya yi, ta imaka matuka wajen kara fito da matsayin addinin musulunci a kasashen turai da ma duniya baki daya, wanda ake kallon hakan a matasayin aikin da ya cancanci yabo.
756130