IQNA

Gangamin Goyon Bayan Masu Bore A Kasashen Larabawa A Birnin Beirut

13:09 - March 02, 2011
Lambar Labari: 2089278
Bangaren siyasa da zamantakewa, wasu gungun matasa a birnin Beirut na kasar Labanan za su gudanar da wani gangami a gaban ofishin jakadancin kasar Yemen da ke birnin, domin nuna goyon bayansu ga masu gudanar da bore a cikin kasashen larabawa, domin kawo karshen mulkin kama karya da suke fama da shi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lebanonfiles an bayyana cewa, wasu gungun matasa a birnin Beirut na kasar Labanan za su gudanar da wani gangami a gaban ofishin jakadancin kasar Yemen da ke birnin, domin nuna goyon bayansu ga masu gudanar da bore a cikin kasashen larabawa, domin kawo karshen mulkin kama karya da suke fama da shi daga azzaluman mahukuntansu da sarakunansu.
Matasan za su gudanar da gangamin a gaban ofisoshin jakadancin kasashen larabawa da suke fuskantar boren al’ummominsu, wadanda suke neman canji daga mulkin zalunci na shugabannin larabawa, musamman ma kasashen da suka dauki matakin murkushe masu boren da karfin tuwo, inda za su fara da ofishin jakadancin kasar Yeman.
Bayan nan kuma matasan za su nufi ofishin majalisar dinkin duniya da ke birnin, domin nuna rashin amincewarsu da matakin da majalisar take dauka na yin gum da bakinta kan ahkkokin fararen hula matakar dai ba maslahar masu juya ta.
Matasan na lebanon sun yi kakkausar da yin Allawadai da gwamnatocin kasashen Yemen Libya da Bahrain kan kisan gillar da suka yi wa fararen hula masu zanga-zangar lumana.
756108



captcha