Bangaren kasa da kasa, Majami’ar Norway da ke kasar Birtaniya tana shirin fara aiwatar da wani shirin musamman da take da shi na wayar da kai kan manufofin addinin musulunci, tare da bijiro da mahangar majami’ar kan yadda ya kamata a zauna da musulmi lafiya.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na networknowich an bayyana cewa, Majami’ar Norway da ke kasar Birtaniya tana shirin fara aiwatar da wani shirin musamman da take da shi na wayar da kai kan manufofin addinin musulunci, tare da bijiro da mahangar majami’ar kan yadda ya kamata a zauna da musulmi lafiya a fadin kasar ta Birtaniya.
Babbar manufar kirkiro da wannan shirin dai ita ce samar da fahimtar juna tsakanin mabiya addinan musulunci da kuma kiristanci, ta yadda dukkanin bangarorin biyu za su iya gudanar da abubuwa da dama musamman ma kan abubuwan da suka hada su, domin a samu fahimta mai dorewa.
Majami’ar Norway da ke kasar Birtaniya tana shirin fara aiwatar da wani shirin musamman da take da shi na wayar da kai kan manufofin addinin musulunci, tare da bijiro da mahangar majami’ar kan yadda ya kamata a zauna da musulmi lafiya.
756616