IQNA

A Hukumce An Amince Da Kungiyar Nahadat Islami A Tunusiya

11:28 - March 03, 2011
Lambar Labari: 2089593
Bangaren kasa da kasa;Ali Alarid kakakin kungiyar Nahadat Islami a kasar Tunusiya a ranar goma ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ya bada labarin cewa; kungiyar a hukumce an amince da ita bayan shekaru talatin na gwagwarmaya da kuma kafa ta.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Ali Alarid kakakin kungiyar Nahadat Islami a kasar Tunusiya a ranar goma ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ya bada labarin cewa; kungiyar a hukumce an amince da ita bayan shekaru talatin na gwagwarmaya da kuma kafa ta.Ya kara da cewa sun sami izinin ci gaba da ayyukan kungiyarsu daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta Tunusiya kuma ya jinjinawa yayan kungiyar da suka yi shekaru suna kokarin ganin sun cimma nasara da a wannan rana ga shi sun kai da cimma daya daga cikin abubuwan da suka sa gaba.


756479
captcha