IQNA

Za A Gudanar Da Wani Zaman Taro Karawa Juna Sani Kan Addinai A Birtaniya

Bangaren al'adu da fasaha, za a gudanar da wani zaman taro na kasa na karawa juna sani kan addinai na duniya wanda babbar cibiyar kula da harkokin al'adu da addinai ta kasar Bortaniya ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa .



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar bunkasa harkokin al'adun muslunci a kasar Birtaniya cewa, za a gudanar da wani zaman taro na kasa na karawa juna sani kan addinai na duniya wanda babbar cibiyar kula da harkokin al'adu da addinai ta kasar Bortaniya ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin mako mai zuwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai yi dubi ne kan muhimman abubuwan da suka shafi addinai wadanda aka hadu kansu, da kuma abubuwan da addinai suka samu sabani a kansu, da kuma hanyoyin da za a bi wajen samar da hanaya guda ta hada kan mabiya addinan ta yaddamabiyansu za su zauna lafiya da juna.

Za a gudanar da wani zaman taro na kasa na karawa juna sani kan addinai na duniya wanda babbar cibiyar kula da harkokin al'adu da addinai ta kasar Bortaniya ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin London fadar mulkin kasar.

756965