IQNA

Masu Bincike Iraniya Sun Yi Rangandi A Babbar Cibiyar Binciken Musulunci Ta Malazia

Bangaren fikira da ilimi, Wasu daga cikin tawagar malaman jami'oi a Iran sun gudanar da rangandi a wata babbar cibiyar bincike kan ilmomin Musulunci a a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya samu wani rahoto daga wani shafin yanar gizo cewa, Wasu daga cikin tawagar malaman jami'oi a Iran sun gudanar da rangandi a wata babbar cibiyar bincike kan ilmomin Musulunci a a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia da ke daukar nauyin gudanar da tarukan nazari kan ilmomin addinin Musulunci.

A wata zantawa da ta hada Khusro Taqaddusi niya daya daga cikin malaman jami'a na Iran da suke gudanar da wannan rangadi a wannan cibiya, inda ya bayyana cewa, cibiyar tana daya daga cikin cibiyoyi masu muhimmanci da ya taba ziyarta, domin kuwa ta samar da abubuwan bincike kan ilmomin addini masu yawa.

Kasar Malazia dai daya ce daga cikin kasashen da suke taka gagarumar rawa wajen kara fito da matsayin addinin muslunci a duniya ta fuskoki da dama, daga ciki kuwa har da gudanar da irin wadannan ayyuka a irin wadannan cibiyo.

Wasu daga cikin tawagar malaman jami'oi a Iran sun gudanar da rangandi a wata babbar cibiyar bincike kan ilmomin Musulunci a a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia.

757468