IQNA

Taron Malaman Mazhabar Iyalan Gidan Manzon Allah (SAW) Da Kuma 'Yan Sunna A India

14:04 - March 05, 2011
Lambar Labari: 2090418
Bangaren al'adu da fasaha, za a gudanar da wani zaman taro na malaman addinin muslunci da suka hada da malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa, gami da malaman 'yan sunna a kasar India.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Unnao an habarta cewa, za a gudanar da wani zaman taro na malaman addinin muslunci da suka hada da malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa, gami da malaman 'yan sunna a kasar India a wata babbar HusainiyaNewtani.

Bayanin ya ci gaba da cewa a kan shirya gudanar da irin wannan zaman taro domin yin bahasi kan abubuwan da dukkanin bangarori musulmi suka hada a kansu, da kuma yadad za su iya yin aiki tare da juna, da kuma samar da hanyar hada dukkanin mabiya addinin Musulunci na kasar.

Za a gudanar da wani zaman taro na malaman addinin muslunci da suka hada da malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa, gami da malaman 'yan sunna a kasar India.

757119




captcha