Bangaren kasa da kasa, Za agudanar da wani zaman taro kan rayuwar ma’ikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da kuma tarihin addinin musulunci, wanda za a gudanar a birnin paris fadar mulkin kasar faransa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro kan rayuwar ma’ikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da kuma tarihin addinin musulunci, wanda za a gudanar a birnin paris fadar mulkin kasar faransa da zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar.
Muhammad Ghamgue wanda daya ne daga cikin manyan malamai a babbar cibiyar nazarin addinin musulunci ta kasa da kasa da ke birnin na paris, kuma jami’i a cibiyar nazarin halayyar dan adam ta kasashen turai, da daya daga cikin wadanda za su gabatar da jawabai a wajen taron.
Za agudanar da wani zaman taro kan rayuwar ma’ikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da kuma tarihin addinin musulunci, wanda za a gudanar a birnin paris fadar mulkin kasar faransa.
757487