IQNA

Malaman Mazhabar A Kasar Saudiyya Sun Bukaci A Saki Limamin Garin Ihsa

18:28 - March 06, 2011
Lambar Labari: 2091265
Bangaren kasa da kasa, sama malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah dari daya 100 ne suka bukaci da a saki malamanin addini kuma limamin juma’a na garin Ihsa da mahukuntan gidan sauratar mulukiya na Saudiyya suka tsare.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rasid an bayyana cewa, sama malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah dari daya 100 ne suka bukaci da a saki malamanin addini kuma limamin juma’a na garin Ihsa da mahukuntan gidan sauratar mulukiya na Saudiyya suka tsare ba tare da tuhumarsa da aikata wani laifi sai don dalilai na siyasa.
A cikin wani bayani na hadin gwiwa da suka fitar, malaman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon na yankunan Ihhsa da kuma Katif a gabacin kasar Saudiyya, sun kirayi mahukuntan kasar da su kwana da sanin cewa ci gaba da rike shehin malamin na tattare da babban hadari ga zaman lafiyar kasar.
sama malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah dari daya ne suka bukaci da a saki malamanin addini kuma limamin juma’a na garin Ihsa da mahukuntan gidan sauratar mulukiya na Saudiyya suka tsare shi.
757901

captcha