Bangaren siyasa da zamantakewa:Na'im Alkandur shugaban hadin guiwar kungiyoyin musulmi a Girka ya bada labarin kaddamar da wani shafin internet da zai maida hankali wajan yada addinin musulunci a tsakanin al'ummar kasar ta Girka.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Na'im Alkandur shugaban hadin guiwar kungiyoyin musulmi a Girka ya bada labarin kaddamar da wani shafin internet da zai maida hankali wajan yada addinin musulunci a tsakanin al'ummar kasar ta Girka. Wannan shafin internet wata babbar dam ace da za a rika yin bayani dalla-dalla da suka shafi harkokin addinin musulunci da kuma yadda al'ummar wannan kasa za su rika samin labarai da suka shafi addinin musulunci cikin sauki .
758498