IQNA

Ma'ikatar Kula Da Harkokin Addini Ta Palstinu Ta Yi Allawadai Da Rusa Harabar Qods

18:13 - March 07, 2011
Lambar Labari: 2091998
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addini a palastinu ta yi kakkausar suka da kuma yin Allawadai da rusa wani bangare na harabar masallacin Qods mai alfarma da yahudawan sahyuniya suka yi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palasrine info an bayyana cewa ma'aikatar kula da harkokin addini a palastinu ta yi kakkausar suka da kuma yin Allawadai da rusa wani bangare na harabar masallacin Qods mai alfarma da yahudawan sahyuniya suka yi domin tsokanar mabiya addninan kiristanci da kuma musulmi.

Haramtacciyar kasar Isra'ila tana rusa wani bangare na harabar masallacin Qods domin kara fadada bangaren da yahudawan sahyuniya suke da'awar cewa nasu ne, amma hukumar kula da ayyukan addini ta palastinu ta bayyana hakan da cewa wani mataki ne na hankoron mayar da birnin Qods mallakin yahudawa.

A cinin da ma'aikatar kula da harkokin addini a palastinu ta fitar ta yi kakkausar suka da kuma yin Allawadai da rusa wani bangare na harabar masallacin Qods mai alfarma da yahudawan sahyuniya suka yi a cikin kwanakin na.

758690






captcha