Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ra’ay ta kasar Kuwait an bayyana cewa, mataimakin babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki a kasar Kuwait Abdullah Mahdi Barrak ya sheda cewa, ana shirin gudanar da wani babban taro na karawa juna sani kan manufofin tarbiyar kur’ani mai tsarki a cikin rayuwar jama’a ta yau da kullum.
Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la’akarui da cewa wannan shi ne karon farko da za agudanar da irin wannan taro a kasar nan da makonni uku masu zuwa, za agayyaci malamai da kuma masana daga sassa daban-daban na kasar domin su halarta, kuma su gabatar da jawabai kan hakan ga mahalarta.
mataimakin babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki a kasar Kuwait Abdullah Mahdi Barrak ya sheda cewa, ana shirin gudanar da wani babban taro na karawa juna sani kan manufofin tarbiyar kur’ani mai tsarki.
759234