IQNA

Zaman Tattaunawa Tsakanin Kasashen Musulmi Da Kuma Kasar Japan A UAE

19:04 - March 08, 2011
Lambar Labari: 2092720
Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da zaman taro na tattaunawa tsakanin kasashen musulmi da kuma kasar Japan a kasar hadaddiyar daular larabawa, da zai samu halartar jami’ai da kuma masana da za agudanar a babban dakin taruka na jami’ar Zayid da ke birnin Abu Dhabi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkausar an bayyana cewa, za a fara gudanar da zaman taro na tattaunawa tsakanin kasashen musulmi da kuma kasar Japan a kasar hadaddiyar daular larabawa, da zai samu halartar jami’ai da kuma masana da za agudanar a babban dakin taruka na jami’ar Zayid da ke birnin Abu Dhabi fadar mulkin kasar ta hadaddiyar daular larabawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan shi ne karo na farko da za agudanar da wannan zaman taro, wanda yanzu haka bangarorin da za su halarce sun riga sun fara isowa kasar, kuma taron zai fara ne daga daren yau zuwa wasuu kwanaki nan gaba, daga cikin abubuwan da zai yi dubi kansu har da dangantaka ta addini da al’adu tsakanin kasashen musulmi da Japan.
za a fara gudanar da zaman taro na tattaunawa tsakanin kasashen musulmi da kuma kasar Japan a kasar hadaddiyar daular larabawa, da zai samu halartar jami’ai da kuma masana da za agudanar a babban dakin taruka na jami’ar Zayid da ke birnin Abu Dhabi.
759163
captcha