Bangaren kasa da kasa, Mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar China Mawon Bi ya bayyana cewa gwamnatin kasar na shirin kafa wani wurin ajiye kayan tarihin kasar da ska danganci kur'ani mai tsarki, inda za a ajiye wani kwafin kur'ani da aka samu a kasar kimanin shekaru dubu daya da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo naarabic.china an habarta cewa, Mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar China Mawon Bi ya bayyana cewa gwamnatin kasar na shirin kafa wani wurin ajiye kayan tarihin kasar da ska danganci kur'ani mai tsarki, inda za a ajiye wani kwafin kur'ani da aka samu a kasar kimanin shekaru dubu daya da suka gabata da har yanzu yake ajiye a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa an samu wannan kur'ani ne a wani yanki da mabiya addinin Musulunci suke zaune a cikinsa, wanda kuma ko shakka babu hakan ya dauki hankalin mahukuntan kasar ta China, tare da bayyana samun wannan kur'ani a matsayin wani abin alfahari na kasa baki daya.
Mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar China Mawon Bi ya bayyana cewa gwamnatin kasar na shirin kafa wani wurin ajiye kayan tarihin kasar da ska danganci kur'ani mai tsarki, inda za a ajiye wani kwafin kur'ani da aka samu a kasar kimanin shekaru dubu daya da suka gabata.
759906