IQNA

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga A Gabacin Saudiyya

12:41 - March 13, 2011
Lambar Labari: 2094717
Bangaren kasa da kasa, Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah na kasar saudiyya sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a yankunan da ke kudancin kasar, inda suke neman da agudanar da sauye-sauye a cikin harkokin mulki da siyasar kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rasid an bayyana cewa, Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah na kasar saudiyya sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a yankunan da ke kudancin kasar, inda suke neman da agudanar da sauye-sauye a cikin harkokin mulki da siyasar kasar ta Saudiyya wadda ke karkashin mulkin mulikiya na sarakuna sama da shekaru dari biyu da suka gabata.
Tun kimanin makonni biyu da suka gabata ne aka fara gudanar da zanga-zanga a wasu yankuna na kasar saudiyya, musamman a gabacin kasar, domin neman gudanar da sauye-sauye a salon mulkin mulukiyya na Ali-Saud da ke iko kasar, amma mahukuntan na Saudiyya sun dauki tsauraran matakai na ganin cewa wannan bore bai yi tasiri ba, inda jami'an tsaro suka yi amfani da karfin tuwo wajen hana zanga-zanga a yankunan Katif da kuma Awamiyya da Ihsa, da kuma birnin Riyad.
Jami'an tsaron na Saudiyya sun afka kan wata zanga-zangar da daruruwan mata suka gudanar a garin Dammam, domin neman sakin mazajensu da 'ya'yansu da mahukuntan kasar ke tsare da su saboda dalilai na siyasa, inda jami'an tsaron suka yi ta kwada musu kulake da kuma jefa barkonon tsohuwa a kansu.
Ita kuwa gamayyar kungiyoyin matasan kasar ta Saudiyya ko (shaba al-ahrar) ta yi kira ne ga dukkanin al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar juma'a mai zuwa, domin gudanar da gagarumar zanga-zangar neman sauyi, lamarin da ga dukkan alamu ya kada hantar mahukuntan kasar ta Saudiiya, inda suka sanar da kafa dokar hana fita a ranar Juma'a mai zuwa fadin kasar baki daya.
Kuma an baza jami'an tsaro a mafi yawan garuruwan kasar a cikin shirin ko ta kwana, domin murkushe duk wata zanga-zangar nuna kyama ga gwamnati, a daidai lokacin da gamayyar kungiyoyin matasan da kuma bangarorin 'yan adawa suka jaddada cewa babu gudu babu ja da baya kan gudanar da zanga-zagar da suka shirya.
Ganin haka ne ma ya sanya malaman gwamnatin Saudiyya kamar dai yadda suka saba, ba su yi wata-wata ba wajen fitar da fatawar haramta gudanar da duk wani gangami ko zanga-zagar nuna kyama ga mahukuntan kasar, lamarin da ya fuskanci mayar da martani daga al'ummomin musulmi da na larabawa.
761871

captcha