Bangaren al'adu da fasaha, An fara gudanar da wani zama da aka yi wa take da makon al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Birtaniya, wanda ofishin hukumar kula da ayyukan al'adun Musulunci da bunkasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, a fara gudanar da wani zama da aka yi wa take da makon al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Birtaniya, wanda ofishin hukumar kula da ayyukan al'adun Musulunci da bunkasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin na London.
A Wani bangare kuma Iran ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hakar danyen mai a manyan rijiyoyin hakar mai biyu da ke yankin Azarbaijan.
Mataimakin ministan main a kasar Iran ya sheda cewa, akwai aikace-aikace da bangarorin biyu za su gudanar a wadannan manyan rijiyoyin mai biyu, wanda hakan zai lakume kudi har dalar Amurka biliyan shida.
Ya ce sakamakon kakaba takunkumin karya tattalin arziki da kasashen yammacin turai suka yi kan Iran, hakan ya ba ta damar ci gaba da dogara da kanta a cikin harkoki da dama, musamman ma bangaren da kamfanonin kasashenturai suka janye, duk da cewa akwai kasashe masu 'yancin siyasa da suke ci gaba da kara bunkasa harkokin tattalin arzikinsu da kasuwanci tare da Iran.
762024