IQNA

Limamin Juma’a A Katif Ya Yi Kakkausar Suka Kan Mahukuntan Kasar Saudiyya

14:53 - March 14, 2011
Lambar Labari: 2095726
Bangaren kasa da kasa, wanda ya jagoranci sallar juma’a a garin Katif da ke gabacin kasar Saudiyya ya yi kakkausar suka kan irin matakan zalunci da danniya da da suke dauka kan masu gudanar da zanga-zangar neman sauyi a kasar, musamman wadanda suke a yankunan gabacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar sadarwa na rasid cewa, wanda ya jagoranci sallar juma’a a garin Katif da ke gabacin kasar Saudiyya ya yi kakkausar suka kan irin matakan zalunci da danniya da da suke dauka kan masu gudanar da zanga-zangar neman sauyi a kasar, musamman wadanda suke a yankunan gabacin kasar wadanda mabiya mazhabar iyalan gidan manzon zo ne.
Tun kimanin makonni biyu da suka gabata ne masu fafutuka da kuma kungyoyin farar hula da na matasa a kasar Saudiyya, suka bukaci gudanar da zanga-zangar lumana a kasar domin neman sauyi a cikin harkokin mulkin kasar, wadda ta kwashe tsawon shekaru tana fama da mulkin mulukiya na gidan sarautar ali Saud da ‘yan mulkin mallakar Birtaniya suka kafa.
wanda ya jagoranci sallar juma’a a garin Katif da ke gabacin kasar Saudiyya ya yi kakkausar suka kan irin matakan zalunci da danniya da da suke dauka kan masu gudanar da zanga-zangar neman sauyi a kasar, musamman wadanda suke a yankunan gabacin kasar.
762558

captcha