IQNA

An Gudanar Taron Tunawa Da Zagayowar Ranar Maulidin Imam Hassan Askari (AS) A India

Bangaren al’adu da fasaha, An gudanar da zaman taro na tunawa da ranar haihuwar Imam Hassan Al-askari limami na goma sha daya daga cikin limaman iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a kasar India.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wanmi labari da ya nakalto daga wani shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, An gudanar da zaman taro na tunawa da ranar haihuwar Imam Hassan Al-askari limami na goma sha daya daga cikin limaman iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a kasar India da ya samu halaratar masana da malamai.
Al’umma ba ta yi tarayya kan daukakar wasu mutane ba kamar yadda ta yi tarayya kan daukakar shugabannin shiriya na iyalan gidan Manzon Allah {S.A.W}. Hakika al’ummar da ta gabata da ta yanzu, sun yi tarayya kan daukakar matsayin zuriyar Manzon Allah tsarkaka, tare da maganganu kan girman matsayinsu da daukakarsu, kuma malaman musulunci da na sauran addinai sun yi rubuce- rubucen yabo kansu, inda suka ambaci kyawawan dabi’unsu da daukakarsu a kan sauran mutane. Watakila rubuce-rubucen da malaman Ahlus-sunnah suka yi kan shugabannin shiriya na Iyalan gidan Manzon Allah a littattafansu sun fi na mabiyansu yawa, wanda hakan ba abin al’ajabi ba ne idan aka yi la’akari da yadda malaman musulunci suka ruwaito tarin hadisan da Manzon Allah {S.A.W} yayi wasici da su ga al’umma a bayansa, bayan da ya rubanyasu da alkur’ani mai tsarki saboda tsarkinsu.
Don haka zamu ambaci kadan daga cikin maganganun yabo da malamai da sauran mutanen da suka rayu tare da Imam Hasan Al-Askari {A.S} suka yi kansa kamar haka.
Ibnu Sabbaghil Maliki a cikin littafinsa na Fusulul-Muhimmah yana cewa: Imam Hasan Al-Askari {A.S} shi ne shugaban al’ummar zamaninsa kuma jagoran shiriya a lokacinsa, mai gaskiyar zance da ayyuka abin godiya. Idan madaukaka a zamaninsa sun kasance masu zurfin tunani, to shi ne tushen tunani da hankali, shi ne mai zurfin ilimi da ba shi da makamanci, mai bayyana abubuwan da suka shige wa mutane duhu, kuma babu mai iya jayayya ko musu da shi, mai fayyace hakikanin abubuwa da zurfin hangen nesa, mai bayyana abubuwa masu zurfi da kaifin tunaninsa, mai kyakkyawan asali da tsarkakan zuciya.
Sibdi Bin Jauzi a cikin littafinsa na Tazkiratuz-Khawas yana cewa: Shi ne Hasan Dan Ali Dan Muhammad Dan Ali Dan Musa Dan Ja’afar Dan Muhammad Dan Ali Dan Husaini Dan Ali Dan Abi-Talib {A.S} wanda ya kasance masani amintacce da ya ruwaito hadisai daga mahaifinsa da kakansa.
Ya zo cikin littafin It'haf-bi-Hubbil-Ashraf Allamah Asshibrawiyyu Asshafi’i yana cewa: Jagora na goma sha daya daga cikin jagororin shiriya na iyalan gidan manzon Allah {S.A.W} shi ne: Hasan Al-khalis kuma ana masa lakabi da Al-Askari, kuma ya ishe shi daukaka kasancewar Mahdi da ake jiran bayyanarsa daga cikin ya'yansa, wallahi daga Allah ne alkhairin da yake fitowa daga wannan gida madaukaki.
Yusuf Isma’il Annabhani a cikin littafin Jami’u-Karama’tul-Auliya’i yana cewa: Hasan Al-Askari daya ne daga cikin jagororin shiriya kuma shugabannin iyalan gidan manzon Allah masu girma {R.A}.
762447