Bangaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta aike da sako na musamman da ke isar da ta'aziyya ga al'ummar kasar Japan kan baa'in girgizar kasar da ya afku a kasar, wanda ya yi sanadiyar dubban mutane.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC an bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta aike da sako na musamman da ke isar da ta'aziyya ga al'ummar kasar Japan kan baa'in girgizar kasar da ya afku a kasar, wanda ya yi sanadiyar dubban mutane wasu da dama kuma suka samu raunuka, yayin da wasu kuma suka bata cikin ruwa ko kuma suka rasa gidajensu.
Masana kan harkokin girgizar kasa sun bayyana cewa karfin girgizar kasar da ta afku a kasar Japan a ranar Juma'ar da ta gabata ya kai maki 9.2 a ma'aunin ritcher, wanda mahukuntan kasar suka bayyana shi da cewa ya fi muni akan dukkanin wadanda kasar ta taba gani a cikin tarihinta.
kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta aike da sako na musamman da ke isar da ta'aziyya ga al'ummar kasar Japan kan baa'in girgizar kasar da ya afku a kasar, wanda ya yi sanadiyar dubban mutane.
763247