Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na mabiya addinin musulunci a yankin Rajuri na yankin keshmir, wanda ya samu halartar daruruwan malaman addini da kuma mutanen yankin wadanda akasarinsu mabiya addinin musulunci ne.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Greater Kashmir an habarta cewa, an gudanar da wani zaman taro na mabiya addinin musulunci a yankin Rajuri na yankin keshmir, wanda ya samu halartar daruruwan malaman addini da kuma mutanen yankin wadanda akasarinsu mabiya addinin musulunci ne da suke fuskantar matsaloli da mahukuntan kasar India.
Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da wannan zaman taro ne da nufin kara karfafa mabiya addinin musulunci kan sanin addininsu da kuma tarihin manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa, wanda hakan ne zai ba su damar yin aiki da koyarwa a cikin dukkanin harkokinsu na rayuwar zamantakewa.
An gudanar da wani zaman taro na mabiya addinin musulunci a yankin Rajuri na yankin keshmir, wanda ya samu halartar daruruwan malaman addini da kuma mutanen yankin wadanda akasarinsu mabiya addinin musulunci ne.
764153