Bangaren kasa da kasa, za a kafa wani kwamiti na mabiya addinin mulunci a kasar Switzerland, wanda zai rika yin dubi kan dukkanin harkokin musulmi da suka shafi rayuwarsu ta zamantakewa a kasar, da kuma hakkokinsu da 'yancinsu na addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na journaldujura an bayyana cewa, za a kafa wani kwamiti na mabiya addinin mulunci a kasar Switzerland, wanda zai rika yin dubi kan dukkanin harkokin musulmi da suka shafi rayuwarsu ta zamantakewa a kasar, da kuma hakkokinsu da 'yancinsu na addini wanda babbar cibiyar musulmi ta kasar ta shiga gaba wajen ganin an kafa tare da yi masa rijista a hukumance.
Al'ummar musulmin kasar Switzerland wadanda akasarinsu larabawa ne daga kasashen arewacin Afirka da kuma gabas ta tsakiya, gami da turkawa da kuma bakaken fata, suna fuskantar matsaloli a wasu lokuta dangane da lamurran addininsu, inda akwanakin baya mahukuntan kasar suka kafa dokar hana gina masallatai a kasar, a matsayin wani mataki na nuna wariya ga mabiya addinin Musulunci.
Kafa wani kwamiti na mabiya addinin mulunci a kasar Switzerland, wanda zai rika yin dubi kan dukkanin harkokin musulmi da suka shafi rayuwarsu ta zamantakewa a kasar, da kuma hakkokinsu da 'yancinsu na addini, zai baiwa musulmin damar gudanar da harkokinsu cikin 'yanci.
763912