IQNA

Pira Ministan Kasar Turkiya Ya Bayyana Cewa Ba A Fatan A sMaimaita Wata Karbala

18:33 - March 17, 2011
Lambar Labari: 2097314
Bangaren siyasa da zamantakewa, pira ministan kasar Turkiya Rajad Tayyib Ardugan ya bayyana cewa, ba fatan a sake maimaita wata karbala a wannan zamani, a lokacin da yake yin ishara da kisan kiyashin da azzaluman shugabanni da sarakunan larabawa suke kan al'ummominsu a wannan zamani.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, pira ministan kasar Turkiya Rajad Tayyib Ardugan ya bayyana cewa, ba fatan a sake maimaita wata karbala a wannan zamani, a lokacin da yake yin ishara da kisan kiyashin da azzaluman shugabanni da sarakunan larabawa suke kan al'ummominsu a wannan zamani.

A bangare guda kuma Aummomin kasashen larabawa na ci gaba da yin kakausar mahukuntan kasar Saudiyya, bayan da suka tura sojoji da kayan yaki zuwa kasar Bahrain, domin murkushe fararen hula da ke zanga-zangar lumana a kasar.

Babban malamin addinin Musulunci a kasar Iraki Ayatollah Ozma Sayyid Ali Sistani, ya bayyana matakin da gwamnatin Saudiyya ta dauka na shiga cikin kasar Bahrain domin murkushe fararen hula masu neman sauyi da cewa babban kuskure ne A nasu bangaren 'yan majalisar dokokin kasar Kuwait sun ja kunnen sarkin kasar da a hir dinsa ya bi sahun gwamnatin Saudiyya wajen aikewa da dakaru zuwa kasar Bahrain domin murkushe zanga-zangar lumana, idan kuma ya yi hakan ya kwana da sani cewa za su dauki matakan ladabtar da gwamnati, lamarin da ya tilasta sarkin na Kuwait canja shawara.

Kungiyoyin farar hula gami da jam'iun siyasa da kuma kungiyoyin lauyoyi 769 ne a kasashen larabawa daban-daban suka fitar da bayanin yin Allawadai da mahukuntan Saudiyya, tare da bayyana shisshigin da ta ke yi kan al'ummar kasar Bahrain da cewa ya saba wa dukkanin ka'idoji da dokoki na kasa da kasa, wasu daga cikin kungiyoyin palastinawa kuwa sun bayyana cewa, sama da shekaru 60 HKI na yin musu kisan gilla ba taba jin mahukuntan Saudiyya sun yi ko da Allawadai ne da hakan ba, balantana ma su taimaka musu, amma ta tura sojoji domin kashe musulmi larabawa masu neman sauyi a Bahrain.

764972

captcha