IQNA

Kardawi Ya Yi Gargadi Dangane Da Kisan Masu Bore A Kasar Yeman

18:36 - March 17, 2011
Lambar Labari: 2097316
Bangaren kasa da kasa, babbar kungiyar gamayyar malaman addinin Musulunci ta kasa da kasa ta yi kakkausar suka dangane da kisan gillan da ake yi kan fararen hula masu bore a kasar Yeman, tare da kiran mahukuntan kasar da su saurari abin da masu zanga-zangar ke fada ko suke nema maimakon mayar musu amsa da harsasan bindiga.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkausar an bayyana cewa, babbar kungiyar gamayyar malaman addinin Musulunci ta kasa da kasa ta yi kakkausar suka dangane da kisan gillan da ake yi kan fararen hula masu bore a kasar Yeman, tare da kiran mahukuntan kasar da su saurari abin da masu zanga-zangar ke fada ko suke nema maimakon mayar musu amsa da harsasan bindiga da yin kisan gilla a kansu.

Rahotanni daga kasar Bahrain sun tabbatar da cewa fararen hula shida ne sojojin kasar da na Saudiyya suka kashe a jiya Laraba, tare da jikkata wasu sama da 400.

Shedun gani da idon sun tabbatar da cewa a jiya sojojin Saudiyya sun kai hari kan dubban fararen hula da ke zanga-zangar lumana a Bahrain, inda suka kashe mutane biyar suka jikkata wasu sama da 400, haka nan kuma sojin na Saudiya sun kan wani harin kan asibitin Sulaimaniyya da ke cikin birnin Manama, inda suka kashe wani farar hula har lahira, kuma suka kuma kore dukkanin marassa lafiya sama da dubu daya dake kwance a asibitin, bisa hujjar cewa a nan ake wa masu zanga-zanga magani idan suka samu raunuka, ko ajiye gawawwkin wadanda suka mutu daga cikinsu, wanda hakan kan ba 'yan jaridar damar sanin adadin mutanen da aka kashe ko raunatawa.

A jiya an gudanar da gangami a kasashen larabawa daban-daban domin yin Allawadai da mahukuntan Saudiyya, kan kisan gillar da suke yi kan al'ummar kasar Bahrain marassa kariya, daga cikin kasashen da aka gudanar da gangamin har Iraki, Lebanon, Tunisia, Syria da kuma yankunan gabacin kasar ta Saudiyya.

765097




captcha