IQNA

Son Addinin Musulunci Da Neman Adalci Shi Ne Ruhin Motsin Al'ummomin Larabawa

18:15 - March 19, 2011
Lambar Labari: 2097591
Bangaren siyasa da zamantakewa, wanda ya jagoranci sallar juma'a a birnin Tehran Ayatollah Ahmad Jannati ya bayyan acewa, son addinin Musulunci da kuma kumajin ganin an tabbatar da adalci , shi ne babban ruhin motsin da ake gani a yankin gabas ta tsakiya da ma kasashen arewacin nahiyar Afirka.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Wanda ya jagoranci sallar juma'ar da aka gudanar a yau a nan birnin Tehran Ayatullah Ahamad Jannati ya bayyana cewa ko shakka babu kasar Amurka ce kanwa uwar gami dangane da yadda ake zubar da jinin jama'ar da ke neman sauyi a kasashe da dama na yankin Gabas ta Tsajkiya.
Ayatullah Jannati wanda yake gabatar da hudubar sallar juma'ar a masallacin jami'ar birnin Tehran a yau din nan, ya ce halayen da gwamnatin kasar Amurka take nunawa dangane da yadda ake afka wa masu zanga-zanga daga wannan kasa zuwa waccan a cikin yankin na Gabas ta tsakiya, wani babban misali ne da ke kara tabbatar wa duniya cewa Amurkar tana da hannu a game da irin dirar mikiyar da jami'an tsaro ke yi wa jama'a a wadannan kasashe.
Wanda ya jagoranci sallar juma'ar a nan birnin Terhran ya bayar da misali da abubuwan da ke faruwa a kasar Bahrain inda gidan sauratar tsirarru 'yan Sunna ke hana wa 'yan Shi'a masu rinjaye a kasar damar fitowa domin bayyana ra'ayoyi, inda limamin ya yi kakkausar suka ga kasashen da ke kiran kansu masu kare demokradiyya kamar dai Amurka, a game da yadda suka zura ido masarautar Saudiyya ta tura dubban sojojinta zuwa kasar ta Bahrain da nufin murkushe masu zanga-zanga duk kuwa da cewa hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.

765504









captcha