IQNA

An Buga Kwafin Littafin Mahdawiyya Guda Dubu 50 Domin Ranakun Nourooz

Bangaren al'adu da fasaha, An buga wani littafi kan akidar nan ta bayyanar mai shiryarwa a karshen zamani da zai cika duniya da adalci bayan cika da zalunci da danniya, wanda musulmi suka yi imani da cewa shi ne mahdi, domin rabawa a cikin ranakun idin norouz.

Bangaren yad alabarai na kamfanin dillancin labaran iqna daga birnin Qom ya habarta cewa, An buga wani littafi kan akidar nan ta bayyanar mai shiryarwa a karshen zamani da zai cika duniya da adalci bayan cika da zalunci da danniya, wanda musulmi suka yi imani da cewa shi ne mahdi, domin rabawa a cikin ranakun idin norouz a cikin fadin jamhuriyar Musulunci.

A bangare guda kuma rahotanni daga birnin Manama na kasar Bahrain sun habarta cewa dakarun mamayar Saudiyya da suka shiga cikin kasar na ci gaba da cin zarafin fararen hula.

Ma'aiko ma gidan talabijin al'alam rahotanni daga birnin Manama ya sheda cewa, sojojin Saudiyya sun kai farmaki kan asibitin Sulaimaniyya da ke tsakiyar birnin, inda aka kwantar da fararen hula sama da dubu daya da suka samu raunuka ko kuma suka rasa rayukansu a zanga-zangar lumana da a'ummar kasar ke gudanarwa domin neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar.

Rahoton ya ce sojojin Saudiyya tare da na Bahrain sun lakada wa wasu likitoci duka, saboda taimaka ma mutane da suke yi a wannan asibiti, daga bisani kuma suka yi awon gaba da su, haka nan kuma sun yanke wutar lantarki da ruwan sha, kamar yadda suka hana isar da magunguna ga marrasa lafiyya ko kula da su, sun kuma kwashe daruruwan marassa lafiya kuma ba san inda suka nufa da su ba.

Al'ummomi da dama a kasashen musulmi da na larabawa suna ci gaba da gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da sarakunan Ali-saud da ke mulki a Sadiyya, sakamakon kisan kiyashin da suke yi kan fararen hula a cikin kasar.

765836