IQNA

Jagoran Juyi Ya Kira Shekarar 1390 Da Shekarar Kwazo Da Bunkasa Tattalin Arziki

15:31 - March 22, 2011
Lambar Labari: 2097821
Bangaren siyasa, a dadidai lokacin da aka shiga shekarar ta 1390, jagoran juyin juya halin musulunci a Iran a cikin sakon sabuwar shekarar shamsiyya da ya aike zuwa ga al’ummar kasar Iran ya saka wa shekarar suna na kwazo da bunkasa harkokin tattalin arzikin kasa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagoran juyin juya halin musulunci cewa, a dadidai lokacin da aka shiga shekarar ta 1390, jagoran juyin juya halin musulunci a Iran a cikin sakon sabuwar shekarar shamsiyya da ya aike zuwa ga al’ummar kasar Iran ya saka wa shekarar suna na kwazo da bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar baki baki daya.
Bayanin ya ci gaba da cewa jagoran ya taya dukkanin al’ummar kasar murnar shiga sabuwar shekara, tare yin fata daga Allah madaukakin sarki da ya yi baiwa ga wannan al’umma ta musulmi a fadin duniya, tare da yin yin kira ga dukkanin al’ummar Iran da su mike tsaye wajen kara himma domin ci gaban kasarsu da al’ummarsu, ta hanyar bunkasa tattalin arziki da kuma yin aiki da koyarwar addini.
Dangane da abubuwan da ke faruwa a kasashen musulmi kuwa na yunkurin neman sauyi kan lamurra na siyasa da kuma kawo karshen tsarin danniya kama karya a kan al’umma wanda shugabanni da sarakuna ke yi musamman ma a cikin kasashen larabawa, ya jadda cewa hakkin al’ummomi ne su nemi hakkokinsu da aka tauye musu daga shugabanni ‘yan kama karya.
A dadidai lokacin da aka shiga shekarar ta 1390, jagoran juyin juya halin musulunci a Iran a cikin sakon sabuwar shekarar shamsiyya da ya aike zuwa ga al’ummar kasar Iran ya saka wa shekarar suna na kwazo da bunkasa harkokin tattalin arzikin kasa.
765868


captcha