Bangaren zamantakewa, Daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci na kasar Iran Ayatollah Mohammad Baqer Shirazi ya bayyana cewa wajibi a nuna cikakken goyon baya ga al’ummar musulmi da suke fuskantar danniya da zalunci daga mahukuntan kasashensu,musamman ma al’ummar Bahrain.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyan a cewa, daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci na kasar Iran Ayatollah Mohammad Baqer Shirazi ya bayyana cewa wajibi a nuna cikakken goyon baya ga al’ummar musulmi da suke fuskantar danniya da zalunci daga mahukuntan kasashensu,musamman ma al’ummar Bahrain da suke fuskantar zalunci da danne hakkokinsu daga azzaluman mahukuntan kasar saboda su mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah ne.
Shehin malamin ya ci gaba da cewa, bisa la’akari da matsayin da kasashen duniya da dama suka dauka dangane da batun yunkurin da al’ummomin kasashen larabawa suke yi domin neman sauye-sauye a cikin harkokin siyasar karasu, inda suke fuskantar zalunci daga shugabanni ‘yan barandan Amurka, ya zama wajibi a nuna goyon baya gare su, tare da yi musu addu’a.
Daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci na kasar Iran Ayatollah Mohammad Baqer Shirazi ya bayyana cewa wajibi a nuna cikakken goyon baya ga al’ummar musulmi da suke fuskantar danniya da zalunci daga mahukuntan kasashensu,musamman ma al’ummar Bahrain. 765882