Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana matukar takaicinsa dangane da yadda wasu bangarori suke ta kokarin danganta batun rikicin kasar Bahrain da sunna shi'a, wanda kuma hakan shi ne tarkon da Amurka ta dana kuma suka fada cikinsa.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana matukar takaicinsa dangane da yadda wasu bangarori suke ta kokarin danganta batun rikicin kasar Bahrain da sunna shi'a, wanda kuma hakan shi ne tarkon da Amurka ta dana kuma suka fada cikinsa ko sun sani ko ba su sani ba.
A bangare guda kuma byanin ya ci gaba da cewa jagoran ya taya dukkanin al’ummar kasar murnar shiga sabuwar shekara, tare yin fata daga Allah madaukakin sarki da ya yi baiwa ga wannan al’umma ta musulmi a fadin duniya, tare da yin yin kira ga dukkanin al’ummar Iran da su mike tsaye wajen kara himma domin ci gaban kasarsu da al’ummarsu, ta hanyar bunkasa tattalin arziki da kuma yin aiki da koyarwar addini.
Dangane da abubuwan da ke faruwa a kasashen musulmi kuwa na yunkurin neman sauyi kan lamurra na siyasa da kuma kawo karshen tsarin danniya kama karya a kan al’umma wanda shugabanni da sarakuna ke yi musamman ma a cikin kasashen larabawa, ya jadda cewa hakkin al’ummomi ne su nemi hakkokinsu da aka tauye musu daga shugabanni ‘yan kama karya.
A dadidai lokacin da aka shiga shekarar ta 1390, jagoran juyin juya halin musulunci a Iran a cikin sakon sabuwar shekarar shamsiyya da ya aike zuwa ga al’ummar kasar Iran ya saka wa shekarar suna na kwazo da bunkasa harkokin tattalin arzikin kasa.
640822