IQNA

An Fitar Da Sabon Bugu Na Mujallar Al-tahira A Cikin Harshen Larabci

15:19 - March 24, 2011
Lambar Labari: 2097922
Bangaren kasa da kasa, an buga sabon buggu na mujallar Al-tahira a cikin harshen larabaci, wanda cibiyar bunkasa harkokin musulunci da ke karkashin cibiyar bunkasa harkokin al’adun musulunci ta dauki nauyin bugawa da yada a cikin kasashen musulmi, wadda ta kunshi shafuka hamsin da shida.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a wani labari da ya naklato daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran an bayyana cewa, an buga sabon buggu na mujallar Al-tahira a cikin harshen larabaci, wanda cibiyar bunkasa harkokin musulunci da ke karkashin cibiyar bunkasa harkokin al’adun musulunci ta dauki nauyin bugawa da yada a cikin kasashen musulmi, wadda ta kunshi shafuka hamsin da shida 56.
Wani labarin kuma ya nuni da cewa an gudanar da wani zaman taro na makon hadin kai tsakanin al’ummar musulmi a babban masallacin Hifield da ke cikin birnin harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a mahangar marigayi Imam Khomeini (RA) daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka.
Bayanin ya ci gaba da cewa, zaman taron wanda aka gudanar a birnin Harare, ya samu halartar mutane da suka hada malamai da kuma sauran mabiya a ddinin musulunci mazauna kasar da kuma ‘yan asalin kasar,inda suka saurari bayanai da aka gabatara wajen taron.
An gudanar da wani zaman taro na makon hadin kai tsakanin al’ummar musulmi a babban masallacin Hifield da ke cikin birnin harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a mahangar marigayi Imam Khomeini (RA) daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidi.
765182

captcha