Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani labari daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, sama da mutane dubu hudu ne aka aike zuwa yankuna daban-daban na kudancin jamhiriyar muslunci domin gudanar da ayyukan taimako ga dukkanin masu bukatr taimako a bangarori na rayuwa musamman ma marassa galihu daga cikinsu.
A wani labarin kuma da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine info an bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar da wani bayani da a cikinsa take bayyana halin da al’ummar yankin Gaza suke ciki na kunci, da hakan ya hada da rashin wutar lantarki da kuma karancin tsaftataccen ruwan sha a yankin.
Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la’akari da yadda haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya ta saka al’ummar yanki cikin wani yanayi na kurkuku, yanayin rayuwarsu sai kara zama cikin muni yake yi, domin kuwa yanzu haka akwai wasu asibitoci da suek fama da karancin magunguna, kamar yadda wutar lantarki a yankin har yanzu ba ta tabbata ba.
kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar da wani bayani da a cikinsa take bayyana halin da al’ummar yankin Gaza suke ciki na kunci, da hakan ya hada da rashin wutar lantarki da kuma karancin tsaftataccen ruwan sha a yankin.
766089