Bangaren kasa da kasa, mutane da dama ne suka shiga cikin cibiyar bunkasa lamarin hardar kur'ani mai tsarki a kasar hadaddiyar daular larabawa, da nufin samun horo na harda da kuma sanin kaidojin karatun kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na wam an bayyana cewa, mutane da dama ne suka shiga cikin cibiyar bunkasa lamarin hardar kur'ani mai tsarki a kasar hadaddiyar daular larabawa, da nufin samun horo na harda da kuma sanin kaidojin karatun kur'ani mai tsarkia kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar kaf awannan kwamiti ita ce samar da hanya mafi inganci wajen buga kwafi-kwafi na kur'ani mai tsarki da rage kurakuran da ake samu wajen bugun, wanda hakan ke faruwa ta hanyar injinan da ake yin amfani da su.
Yanzu haka dai an kafa wani kwamiti da rika sanya ido kan ayyukan buga kwafin kur'ani mai tsarki a cibiyoyin buga littafai a aksar Kuwait, domin kucewa buga kur'ani a kan kuskure, wanda hakan kan jawo matsaloli a cikin harkar karatu da kuma bahasi ga daliban kura'ni mai tsarki.
766163