IQNA

Za A Bude Wani Shafin yanar Gizo Na Gasar Kur'ani Ta Kasa Da Kasa A Kuwait

14:49 - March 28, 2011
Lambar Labari: 2098578
Bangaren kasa da kasa, shugaban kwamitin shirya gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait Ali Al-iwadhi ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za a bude wani sabon shafi na gasar karatun kur'ani mai tsarki da nufin kara karfafa gwiwar masu sha'awar shiga wannan gasa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ra'ayi ta kasar Kuwait an habarta cewa, shugaban kwamitin shirya gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait Ali Al-iwadhi ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za a bude wani sabon shafi na gasar karatun kur'ani mai tsarki da nufin kara karfafa gwiwar masu sha'awar shiga wannan gasa ta littafi mai tsarki.

A wani bangare kuma bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar kaf awannan kwamiti ita ce samar da hanya mafi inganci wajen buga kwafi-kwafi na kur'ani mai tsarki da rage kurakuran da ake samu wajen bugun, wanda hakan ke faruwa ta hanyar injinan da ake yin amfani da su.

Yanzu haka dai an kafa wani kwamiti da rika sanya ido kan ayyukan buga kwafin kur'ani mai tsarki a cibiyoyin buga littafai a aksar Kuwait, domin kucewa buga kur'ani a kan kuskure, wanda hakan kan jawo matsaloli a cikin harkar karatu da kuma bahasi ga daliban kura'ni mai tsarki.

766429







captcha