IQNA

Dubban Masu Ziyara Ne Suka Isa Kasa Mai Tsarki Kasar Azbaketan

14:47 - March 28, 2011
Lambar Labari: 2098581
Bangaren kasa da kasa, hukumar kula da ayyukan addinin musulunci ta kasar Azbaketan ta sanar cewa sama mutane dubu uku ne suka isa kasar Saudiyya domin gudanar da ayyukan ibadar umara a cikin watan da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, hukumar kula da ayyukan addinin musulunci ta kasar Azbaketan ta sanar cewa sama mutane dubu uku ne suka isa kasar Saudiyya domin gudanar da ayyukan ibadar umara a cikin watan da ya gabata, wanda hakan ke nuni da irin ci gaban da ake samu ta fuskacin yawaitar masu zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da ayyukan ibada.

A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, al'ummomin musulmi daga sassa daban-daban na duniya suna ci gaba da nuna fushinsu dangane da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu masu kiran kansu malaman kiristanci suka a yi a cikin kasar Amurka a wani mataki na tsokanar mabiya addinin muslunci na duniya.

An gudanar da zanga-zanga da dubban daruruwan mutane suka shiga a cikin kasashen musulmi daban-daban domin yin allawadai da dukkanin wadanda suke d ahannu wajen aikata wannan mummnan aiki, wanda ya yi hannun riga da dukkanin koyarwar addinai na duniya.

Al'ummomin musulmi daga sassa daban-daban na duniya suna ci gaba da nuna fushinsu dangane da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu masu kiran kansu malaman kiristanci suka yi a cikin kasar Amurka a cikin wannan mako.

766398


captcha