IQNA

Shugabannin Kasashen Turkiya Da Pakistan Sun Yi Allawadai Da Keta Alfarmar Kur'ani

20:11 - March 29, 2011
Lambar Labari: 2098885
Bangaren kasa da kasa, shugabannin kasashen Turkiya da Pakistan sun yi Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Amurka, wanda wani la'antacce da ke kiran kansa kirista ya yi domin tsokanar al'ummar musulmi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar iqtisadiyya an habarta cewa, shugabannin kasashen Turkiya da Pakistan sun yi Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Amurka, wanda wani la'antacce da ke kiran kansa kirista ya yi domin tsokanar al'ummar musulmi na fadin duniya baki daya.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ashararin mutum ya yi hakan ne domin kawo karshen duk wani zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinan kiristanci da na Musulunci da suke zaune lami lafiya a kasashe daban-daban na duniya, wanda hakan ke tabbatar da cewa akwai wata manufa da za ta amfanar da yahudawan sahyuniya ta karkashin kasa wajen yin hakan.

Shugabannin kasashen Turkiya da Pakistan sun yi Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Amurka, wanda wani la'antacce da ke kiran kansa kirista ya yi domin tsokanar al'ummar musulmi a ko'ina.

766677

captcha