Bangaren kasa da kasa, ziyarar hubbaren Imam Hussain (AS) a birnin Karbala mai lafarma daya ne daga cikin ayyuka na jaddada alkawalin Ashura, wanda ke bayyana nuna goyon baya da ruhin taimako ga iyalan gidan manzon Allah (SAW) da aka zalunta a wancan lokaci da ya gabata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa an bayyana cewa, daya daga cikin malaman cibiyar ilimi ta Hauza a birnin Qom Sayyid Fadil Aljabiri ya bayyana cewa ziyarar hubbaren Imam Hussain (AS) a birnin Karbala mai lafarma daya ne daga cikin ayyuka na jaddada alkawalin Ashura, wanda ke bayyana nuna goyon baya da ruhin taimako ga iyalan gidan manzon Allah (SAW) da aka zalunta a wancan lokaci da ya gabata kamar dai yadda ya zo a cikin tarihi.
Malamin ya yi ishara da matsayin iyalan gidan manozn Allah da kuma limaman shirya da smanzon tsira ya yi bushara da bayyanarsu a bayansa, domin ci gaba da isar da sakonsa da Allah ya aiko da shi zuwa ga dam domin fitar da shi daga duhun jahilci da bata da dimuwa, zuwa ga hasken shiriya na iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa.
Malamin ya tabbatar da cewa ziyarar hubbaren Imam Hussain (AS) a birnin Karbala mai lafarma daya ne daga cikin ayyuka na jaddada alkawalin Ashura, wanda ke bayyana nuna goyon baya da ruhin taimako ga iyalan gidan manzon Allah (SAW) da aka zalunta a wancan lokaci da ya gabata. 763758