Bangaren al'adu da fasaha, kimanin mutane miliyan goma ne suka ziyarci masallacin Jamkaran da ke birnin Qom mai alfarma, inda suka duba bajen kolin kayan addini da aka yi a wurin, da suka danganci matsayin limaman tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) da kuma raya tunanin bayyana Imam Mahdi (AJ)
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na banagaren yada labarai na birnin Qom cewa kimanin mutane miliyan goma ne suka ziyarci masallacin Jamkaran da ke birnin Qom mai alfarma, inda suka duba bajen kolin kayan addini da aka yi a wurin, da suka danganci matsayin limaman tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) da kuma raya tunanin bayyana Imam Mahdi Allah ya gaggauta bayyanarsa.
Baje kolin wanda daya ne daga cikin muhimman ayyukan da ake gudanarwa a wannan masallaci mai albarka a kowace shekara, musamman ma a farkon shekara ta hijira shamsiyya, inda miliyoyin mutane suke kai ziyara da kuma ganewa idanunsu sabbin ababen da aka kawo a baje kolin, wanda yake samun karbuwa a kowace shekara daga mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah.
Kimanin mutane miliyan goma ne suka ziyarci masallacin Jamkaran da ke birnin Qom mai alfarma, inda suka duba bajen kolin kayan addini da aka yi a wurin, da suka danganci matsayin limaman tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) da kuma raya tunanin bayyanar Imam Mahdi (AJ) da kuma raya tafarkinsa.
767669