Bangaren kasa da kasa: manbobin komitin koli na Azhar a kasar Masar sun gudanar da wata gagaramar zanga-zanga a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira inda suka bukaci Ahmad Altaib Sheikhul Azhar da sauran jami'an jami'ar da ked a dangantaka da tsohuwar gwamnatin da ta shude da su yi marabus.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ikna ta watsa rahoton cewa; manbobin komitin koli na Azhar a kasar Masar sun gudanar da wata gagaramar zanga-zanga a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira inda suka bukaci Ahmad Altaib Sheikhul Azhar da sauran jami'an jami'ar da ked a dangantaka da tsohuwar gwamnatin da ta shude da su yi marabus. Wadanda suka gudanar da wannan zanga-zangar sun bukaci shi sheikhul Azhar day a yi marabus din saboda kokarin maido da martabar wannan jami'a da mukamin na Sheikhul Azhar da gwamnatin kasar Masar ke yin amfani da shi domin cimma manufarta ta siyasa.
767999