Bangaren kasa da kasa, majalisar dokokin kasar Iraki ta yi kakkausar suka tare da yin Allawadai da keta alfarmar kur’ani mai tsarki, haka nan kuma ta bukaci dukkanin al’ummomin duniya da su dauki na na bai daya wajen yin Allawadai da wannan mummunan aiki da wasu la’anannu suka aikata a kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar Iraki cewa, majalisar dokokin kasar Iraki ta yi kakkausar suka tare da yin Allawadai da keta alfarmar kur’ani mai tsarki, haka nan kuma ta bukaci dukkanin al’ummomin duniya da su dauki na na bai daya wajen yin Allawadai da wannan mummunan aiki da wasu la’anannu suka aikata a kasar Amurka domin tsokanar al’ummar musulmi ta duniya baki daya.
A wani rahoton kuma wani fitatccen marubuci kuma dan jarida a kasar Amurka, ya bukaci da a yi Allawadai da masu cin zarafin musulmi ta hanyar keta alfarmar littafinsu alkur’ani, wanda wasu daga cikin Amurkawa masu tsananin gaba da addinin muslunci suka yi, wanda ya ce hakan keta alfarmutane biliyan daya da rabi ne a duniya baki daya, domin hakan shi ne adadin musulmi.
Ya kara da cewa dukkanin matakin da ya kamata adauka ya kamata ya zama a hukumance, domin kuwa ladabtar da masu son tayar da hankulan al’ummomin duniya ba su da wani banbanci a cikin wace al’umma ko addini, a hakan babu maganar kyale su domin kawai suna mabiya addinin kirista domin da musulmi ne suka yi haka da tuniya ta shi.
769063