Bangaren kasa da kasa, babban sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya yi Allawadai tare da kakkausar suka kan keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu masu kiran kansa mabiya addinin kirista suka yi a kasar Amurka da nufin cin zarafin addinin Musulunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Kuna an bayyana cewa, babban sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya yi Allawadai tare da kakkausar suka kan keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu masu kiran kansa mabiya addinin kirista suka yi a kasar Amurka da nufin cin zarafin addinin Musulunci, wanda a cewarsa hakan ya yi hananun riga da dukkanin koyarwar addinai.
Domin tattauna wannan batu na cin zarafin addinin Musulunci tare da keta alfarmar kur'ani mai tsarki, bababn sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban ko moon ya zauna tare da jakadun kasashen musulmi da suka hada da Pakistan, Tajikistan, Morocco, da kuma Iran, inda ya sheda musu cewa ba zai taba amincewa da cin zarafin wani addini ba.
babban sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya yi Allawadai tare da kakkausar suka kan keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu masu kiran kansa mabiya addinin kirista suka yi a kasar Amurka da nufin cin zarafin addinin Musulunci.
769720