IQNA

Fadar Vatican Ta Yi Allawadai Da Keta Alfarmar Kur'ani Mai Tsarki

13:41 - April 09, 2011
Lambar Labari: 2102671
Bangaren kasa da kasa, fadar Vatican ta mabiya addnin kirista da ke kasar Italiya ta yi kakkausar da kuma yin Allawadai da mummunan aikin da wasu la'annanu suka yi a kasar Amurka na keta alfarmar kur'ani mai tsarki da suka yi ta hanyar kone shi da wuta.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya naalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alkabs ta kasar Kuwait an habarta cewa, fadar Vatican ta mabiya addnin kirista da ke kasar Italiya ta yi kakkausar da kuma yin Allawadai da mummunan aikin da wasu la'annanu suka yi a kasar Amurka na keta alfarmar kur'ani mai tsarki da suka yi ta hanyar kone shi da wuta tare da daukar hotunan bidiyo.

Bayanin ya ci gaba da cewa, abin da wadannan mutanen da suke kansu malaman addnin kirista suka yi a kasar Amurka na kone kur'ani mai tsarki babban laifi ne kuma hakan bay a cikin koyarwa addnin kirista, a hakan fadar Vatican tana yin Allawadai da hakan da kakkausar murya, tare da yin barranta da wannan mummanan aiki.

Fadar Vatican ta mabiya addnin kirista da ke kasar Italiya ta yi kakkausar da kuma yin Allawadai da mummunan aikin da wasu la'annanu suka yi a kasar Amurka na keta alfarmar kur'ani mai tsarki da suka yi ta hanyar kone shi da wuta.

770553
captcha