IKNA HANYA CE TA ISA ZUWA GA DUNIYAR HAKIKA
Mukaddama:
Kamfanin dillancin labaran harkokin kur'ani na iqna shi ne na farko, kuma kamfanin dillancin labaran da ke kawo rahotanni da suka danganci kur'ani mai tsarki a duniyar musulmi. Babban burinmu ya ginu ne kan kawo labarai da suka danganci kur'ani da kuma lamurra da suka danganci Iran da ma duniya baki daya, kan lamurran siyasa, fasaha, adabi, zamantakewa, ayyukan kur'ani, fikira da ilimi, tare da yin bayani a mtsayi na kasa da kasa kan dukkanin wadannan lamurra.
Takaitaccen Tarihi:
An bude kamfanin dillancin labaran iqna ne a ranar 15 ga watan Ramadan na hijira kamariyya 1424, wanda ya yi daidai da 20 ga watan Aban na hijira shamsiyya 1382, tare da halartar shugaban kasa na wancan lokacin Sayyid Muhammad Khatami. Wadanda suka fara gudanar da aiki a lokacin sun fara ne da nufin ci gaba da bin tafarkin marigayi Imam(RA) da jagoran juyin juya hali da kuma shahidan juyin musulunci. An fara ne da samara da labarai 7 a cikin harshen farisanci a kowace rana.
Manufofi:
1- Yada mahangar kur'ani kan matsayin dan adam a tsakanin al'ummomin duniya.
2- Watsa labaran da suka danganci harkokin kur'ani na cikin kasa da kuma na kasa da kasa.
3- Samar da labarai da suka kebanci kur'ani a dukkanin bangarori.
4- Kwadaitarwa zuwa ga kur'ani a cikin dukkanin lamurra, da suka danganci ilmi, fasaha, al'adu, siyasa, adabi, zamantakewa da dai sauransu.
5- Bayyana tasirin kur'ani a jamhuriyar musulunci ta Iran ga sauran kasashen musulmi.
6- Watsa ilmomin kur'ani zuwa ga sauran sassa na duniya.
7- Kara wa juna sani ta hanyar gogewa tsakanin bangarorin da suka samu dacewa wajen aiwatar da shirye-shirye da suka danganci kur'ani, ciki da wajen kasa.
8- Samar da rayayyen tunani a dukkanin bangarori da za su dogara da koyarwar kur'ani.
Muhimamn Ayyuka:
Ayyukan Iqna za a iya bayyana su kamar haka:
A-samar da labarai a kowace rana da tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafin kamfanin dillancin labaran.
B- Gudanar da zama tare masana da kuma jami'ai, domin fayyace wasu labarai.
C- Fitar da wata nashara ta labarai da ke bayani kan labaran Iqna mai suna (Raiheh) da ke fitowa mako-mako.
D- Mayar da hankali kan daukar cikakkun labarai na kur'ani musamman a kafofin yada labarai na ciki da waje.
E- Shiya gudanar da zama na musamman da ke kunsar masana kan dukkanin labarai da kamfanin dillancin labaran iqna ke bayarwa, tare da tabbatar da gaskiyar labari kafin watsa shi. Yanzu haka dai Iqna na shirin samara da labarai 1200 a kowace rana, a cikin harsuna 35 tare da rassa 30 a cikin gida da kuma 15 a wajen kasar, ana fatan aiwatar da hakan a cikin shekara ta 1390.
Masu gudanar da aiki a karkashin wannan kamfanin dillancin labaran ma'aikata ne da ke kuma mambobi a gungun masu hankoron ganin an yada manufofi da koyarwar kur'ani mai tsarki, daga cikin wadanda suke dafa wa kamfanin domin ganin ya samu nasarar guganar da ayyukansa har da jagoran juyin juya halin musulunci a Iran, da sauran jami'an gwamnatin Iran.
Nasharar da iqna ke fitarwa bayan duk makonni biyu (raiheh) na daga cikin muhimman abubuwan da ke yin karin haske kan wannan kamfanin dillancin labarai da kuma ayyukan da yake gudanarwa. Ta hanyar wannan ne a kan karbi ra'yoyin masu karanta labaran iqna daga dukkanin sassa na duniya, ta hanyoyin wayar tarho da ake bayarwa da kuma adireshin akwatin gidan waya na yanar gizo.
1-Producing news data-x-items and conducting interviews in different fields
2-Holding news analysis sessions and roundtables attended by experts and scholars
3-Producing and issuing IQNA’s bi-weekly news bulletin called “Rayeheh” (sweet smell)
4-Full and special coverage of the national ad international Quranic events