IQNA

Gudanar Da Taro Kan Musulunci Addinin Sulhu Da Zaman Lafiya Da Rayuwa A Ceceniya

Bangaren harkokin kur'ani: taron mai taken musulunci addinin sulhu da rayuwa ne da za a gudanar a watan Urdebehesht na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a jamhuriyar Ceceniya.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; taron mai taken musulunci addinin sulhu da rayuwa ne da za a gudanar a watan Urdebehesht na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a jamhuriyar Ceceniya.Wannan taro karo na hudu zai yi nazari da dubi kan rawar gani da addinin musulunci ke takawa wajan tabbatar da sulhu da zaman lafiya a duniya da kuma kasancewarsa addinin rayuwa.

770793