IQNA

An Yi Allawadai Da Rusa Da Kabrukan Bayain Allah A Kasar Masar

19:48 - April 11, 2011
Lambar Labari: 2104230
Bangaren kasa da kasa, wasu malaman addini muslunci sun fito karara sun bayyana rashin jin dadinsu da matakin da wasu wahabiyawa da ke samun goyon baya kai tsaye daga gwamnatin wahabiyawan saudiyya suka dauka a kasar Masar na rusa kabrukan waliyyai da salihan mutane.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Masar ta Ahram an bayyana cewa, malaman addiunin muslunci na kasashen muslmi sun yi Allawadai da wahabiyawan da suka rusa kabrukan waliyai da salihan mutane a kasar Masar, haka nan kuma a wani bangaren rahoton an bayyana cewa, a cikin wani bayani da ofishin jakadancin kasar Amurka da ke birnin Alkahira na kasar Masar ya fitar, ya yi kakkausar da yin Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu suka yi a kasar Amurka, lamarin da yake fuskantar kakkausar daga al'ummomin duniya musulmi daga cikinsu.
Bayanin ya ci gaba da cewa, abin da wadannan mutanen da suke kansu malaman addnin kirista suka yi a kasar Amurka na kone kur'ani mai tsarki babban laifi ne kuma hakan bay a cikin koyarwa addnin kirista, a hakan fadar Vatican tana yin Allawadai da hakan da kakkausar murya, tare da yin barranta da wannan mummanan aiki.
A cikin wani bayani da ofishin jakadancin kasar Amurka da ke birnin Alkahira na kasar Masar ya fitar, ya yi kakkausar da yin Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu suka yi a kasar Amurka, lamarin da yake fuskantar kakkausar daga al'ummomin duniya baki daya.
771541




captcha