Bangaren siyasa da zamantakewa, ana shirin fara gudanar da wani taro a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia dangane da boren da al’ummomin larabawa suke yi ga azzaluman mahukuntansu a cikin lokutan nan, wanda zai samu halartar wakilan kungiyoyin farar hula da na kare hakkin bil adama.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani taro a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia dangane da boren da al’ummomin larabawa suke yi ga azzaluman mahukuntansu a cikin lokutan nan, wanda zai samu halartar wakilan kungiyoyin farar hula da na kare hakkin bil adama na kasar da masu kasashen ketare.
Babbar manufar gudanar da zaman taron dai ita ce yin nazari da kuma kara wajuna sani kan abubuwan da suke faruwa a kasasashen larabawa na bore da al’ummomi suke yi ga azzaluman shugabanni da sarakuna, wadanda suka kwashe tsawon lokaci suna zaluntar mutanensu tare da uwayen gijinsu na kasashen yammacin turai, haka nan kuma zaman taron zai yi dubi kan halin da ake cikin yankunan palastinawa da yahudawan sahyuniya suka mamaye.
Shirin fara gudanar da wani taro a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia dangane da boren da al’ummomin larabawa suke yi ga azzaluman mahukuntansu a cikin lokutan nan, wanda zai samu halartar wakilan kungiyoyin farar hula da na kare hakkin bil adama na kasar da sauran kasashen musulmi. 772533