Bangaren kasa da kasa, babban abin da ya hada al’ummomin kasashen masar da Iran shi ne son iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayansa, gami da kasantuwarsu masu dadadden tarihi da ala’du a yankin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alkausar an bayyana cewa, shugaban kwamitin kyautata dangantaka tsakanin Iran da Masar Ahmad Gamrawi ya bayyan acewa babban abin da ya hada al’ummomin kasashen masar da Iran shi ne son iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayansa, gami da kasantuwarsu masu dadadden tarihi da ala’du a yankin baki daya.
Ya ci gaba da cewa dukkanin al’ummomin kasashen biyu suna da rawar da za su taka adukkanin bangarori da suka hada yankin, duk kuwa matsalolin da aka yi ta samu a lokutan baya, a lokacin da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar yake mulki, wanda ya mika kasar baki daya yahudawan sahyuniya.
Babban abin da ya hada al’ummomin kasashen masar da Iran shi ne son iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayansa, gami da kasantuwarsu masu dadadden tarihi da ala’du a yankin gabas ta tsakiya.
773863