IQNA

An Buga Sabuwar Mujallar Zamzam Ta harshen Turancin Ingilishi

14:48 - April 14, 2011
Lambar Labari: 2105718
Bangaren kasa da kasa, an buga tare da yada sabuwar mujallar nan ta zamzam a cikin harshen turancin ingilishi, wadda cibiyar bunkasa al’adun musulunci da ilimi take daukar nauyin bugawa da watsawa a cikin kasashen duniya domin amfanin masu fahimtar wannan harshe a duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, an buga tare da yada sabuwar mujallar nan ta zamzam a cikin harshen turancin ingilishi, wadda cibiyar bunkasa al’adun musulunci da ilimi take daukar nauyin bugawa da watsawa a cikin kasashen duniya domin amfanin masu fahimtar wannan harshe a duniya.
A wani bangare kuma an habarta cewa za agudanar da wani zaman taron nazarin muslunci a birtaniya, a yayin gudanar da zama masana da malaman jami’oi za su halarta kuma za su gabatar da laccoci ga mahalrta taron, daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hankali kansu akwai nazari kan matsayin sharia a cikin addinin muslunci, da kuma yadda wannan addini mai tsarki yake kallon rayuwar zamantakewa ta jama’a.
Rahoton ya tabbatar da cewa a cikin wata mai kamawa ne za a gudanar da wani zama na karawa juna sani kan nazarin addinin musulunci, wanda za a gudanar a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar Lise da ke kasar Birtaniya a karon farko a wannan jami’a.
773726


captcha