IQNA

14:47 - April 14, 2011
Lambar Labari: 2105720
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Kuwait tare da halartar makaranta da mahardata daga sassan duniya, musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi, inda suka fara karawa da juna a fagagen da aka ware wa gasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Kuwait tare da halartar makaranta da mahardata daga sassan duniya, musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi, inda suka fara karawa da juna a fagagen da aka ware wa gasa ta duniya.
Bugu da kari kan hakan kuma za a gudanar da gasar karatun kur’ani da harda da ta kebanci daliban jami’a a kasar Malazia, wadda za ta hada har da dalibai ‘yan kasashen ketare da sukae karatu a jami’oi daban-daban na kasar Malazia, da nufin karfafa harkokin kur’ani a tsakanin dalibai na kasar baki daya.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar kaf awannan kwamiti ita ce samar da hanya mafi inganci wajen buga kwafi-kwafi na kur'ani mai tsarki da rage kurakuran da ake samu wajen bugun, wanda hakan ke faruwa ta hanyar injinan da ake yin amfani da su.
Yanzu haka dai an kafa wani kwamiti da rika sanya ido kan ayyukan buga kwafin kur'ani mai tsarki a cibiyoyin buga littafai a aksar Kuwait, domin kucewa buga kur'ani a kan kuskure, wanda hakan kan jawo matsaloli a cikin harkar karatu da kuma bahasi ga daliban kura'ni mai tsarki.
773600

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: