Bangaren kasa da kasa, shugaban kwamitin shiray gasar kur’ani a kasar Kuwait Khalid Barrak ya bayyana cewa, za a gudanar da wani taro domin bayyana shafukan yanar gizo da suka kwazo a bangaren harkokin kur’ani mai tsarki a kasar, domin ba su kyautuka na musamman na karfafa gwiwa domin ci gaba da kokari ta fuskar yanar gizo.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya najkalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Kuwait an bayyana cewa, shugaban kwamitin shiray gasar kur’ani a kasar Kuwait Khalid Barrak ya bayyana cewa, za a gudanar da wani taro domin bayyana shafukan yanar gizo da suka kwazo a bangaren harkokin kur’ani mai tsarki a kasar, domin ba su kyautuka na musamman na karfafa gwiwa domin ci gaba da kokari ta fuskar yanar gizo a bangaren ayuukan da suka shafi kur’ani.
Kungiyar malaman addini na jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ta fitar da wani bayani da ke yin kakkausar suka kan keta alfarmar kur’ani mai tsarki da wasu la’anannu suka yi a kasar Amurka da suna ‘yancin fadar albarkacin baki, da hakan ya hada hakoron tunzura mabiya wasu addinai kan addinin musulunci da mabiyansa.
An gudanar da zanga-zanga da dubban daruruwan mutane suka shiga a cikin kasashen musulmi daban-daban domin yin allawadai da dukkanin wadanda suke d ahannu wajen aikata wannan mummnan aiki, wanda ya yi hannun riga da dukkanin koyarwar addinai na duniya.
Al'ummomin musulmi daga sassa daban-daban na duniya suna ci gaba da nuna fushinsu dangane da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu masu kiran kansu malaman kiristanci suka yi a cikin kasar Amurka a cikin wannan mako.
775527